NDLEA ta kama miyagun kwayoyi da suka kai N5.8b a Legas.

Captagon drugs valued at N5.8 billion and rotor coils concealing the drugs seized by the NDLEA at Apapa Port in Lagos NAN
Captagon drugs valued at N5.8 billion and rotor coils concealing the drugs seized by the NDLEA at Apapa Port in Lagos NAN

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), a ranar Laraba ta sanar da kwace adadi mai yawa na Captagon, nau’in maganin Amphetamine, wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 5.8 a tashar Apapa dake Legas.

Shugaban hukumar ta NDLEA, Brig.-Gen. Buba Marwa, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Legas, ya ce kamen Captagon, tare da wanda ake zargi shine na farko a yankin Saharar Afirka.

Ya ce hukumar a watan Maris na 2021, ta samu bayanai daga abokan huldar ta na kasa da kasa, kan jigilar muggan kwayoyi zuwa Najeriya daga Gabas ta Tsakiya, ta tashar Apapa.

Marwa ya bayyanacewa kwantenar ta ƙetare kasashe uku, kuma an yi lodinsa a wata ƙasa ta Arewacin Afirka, yayin da hukumar ta ci gaba da bibiyar ta, tare da haɗin gwiwar takwarorinta.

Ya bayyana cewa, hukumar (NDLEA), ta yi bincike sosai akan kwantenar a ranar 26 ga watan Agusta, amma ta sami injina guda uku, da ake kira Sanders.

Marwa ya ce idan aka yi la’akari da illar Captagon, za a iya gano cewa ana kokarin kaisu sansanin masu tayar da kayar baya da ‘yan fashi a duk fadin Najeriya.

Ya yaba wa jami’an sa da sauran hukumomin tsaro na tashar jiragen ruwa wadanda suka taimaka wajen katse hanzarinsu, yana mai jaddada cewa hukumar tana kan bin diddigin wadanda ake zargi da hannu wajen shigo da wannan haramtaccen maganin. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here