Darakta Janar na Hukumar Kula Da Masu Bautar Kasa, NYSC, Brig-Gen Shuaibu Ibrahim, ya yi kira ga matasa masu hidimar kasa, da su yi amfani da dammar su wajen inganta hadin kai da dunkulewar Najeriya.
Darakta Janar din ya yi kiran ta bakin Shugabar Hukumar a jihar Kano, Hajiya Aisha Muhammad, yayin bikin rantsar da matasan na rukunin B kashi na 11, a sansanin karbar horo dake Kusalla na yankin karamar hukumar Karaye ta jihar.
A cewarsa “dole ne masu bautar kasa su yi amfani da wannan dama da ke zuwa sau daya a rayuwarsu, wajen kokarin inganta hadin kan kasa”
“A matsayin masu bautar kasa daga kabilu da addinai da wurare daban-daban, dole ne ku taka rawa wajen tabbatar da hadin kan kasa”.
“Ina karfafa muku gwiwar yin mu’amala ta kwarai, da musayar dabarun da za su fadada fahimtarku game da kasarnan da kulla abota mai dorewa”.
“Rantsuwar da ku ka yi ta na da kima. Ina bukatarku da ku rika tunawa da shi, kana ya zame muku jagora a wa’adinku na bautar kasa”.
Ya kuma bukaci su nazarci ka’idoji da dokokin hukumar ta NYSC.
Bugu da kari, ya yi kira da su girmama al’adu da akidun al’ummomin da za su karbi bakuncinsu, tare da bada gudunmuwar da zai samar musu da ci gaba.
Ya kara da cewa, hukumar NYSC ta mayar da hankali sosai wajen aiwatar da shirinta na koyar da sana’o’in hannu.
Da farko, shugabar hukumar ta jihar wadda daraktan sansanin Aliyu Ahmed ya wakilta, ta bukaci masu bautar kasar da su kiyaye matakan yaki da annobar COVID-19.
Ya ce babu wani daga cikin matasan da gwaji ya nuna yana dauke da cutar bayan isarsa sansanin.
Ya kuma tabbatar da cewa babu wata barazana da ake fuskanta a sansanin, amma duk da haka, su ci gaba da kiyaye ka’idojin bada tazara da aka gindaya. (NAN)













































