Kungiyar malaman jami’o’i watau ASUU ta zargi shugaban majalisar wakilan tarayyan Najeriya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da yaudarar ta.
Jaridar Tribune ta rahoto kungiyar ASUU ta na cewa yaudarar da Femi Gbajabiamila ya yi mata, ya jawo aka janye yajin-aikin tsawon watanni takwas.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce shugaban majalisar ya nuna masu gwamnati za ta biya su albashin da suke bi. Emmanuel Osodeke ya ce shugaban majalisar ya yi masu alkawari a rubuce cewa da zarar sun janye yajin-aikinsu, albashinsu na duk watannin za su fito.
Da aka yi hira da shi a ranar Talata, 27 ga watan Disamba 2022, Farfesa Osodeke a Tribune, shugaban ASUU ya ce sun yi maraba da sa bakin majalisa.
Shugaban kungiyar malaman jami’ar ya yi wannan fashin baki ne da aka jefa masa tambaya a game da halin da ASUU ta ke ciki da gwamnatin tarayya.













































