An Kori Malamin Jami’a Saboda Lalata Da Wata Daliba

OAU
OAU

Hukumar gudanarwar Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), dake Ile-Ife, ta kori wani Malami, wanda aka samu da laifin lalata da wata daliba.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Mista Abiodun Olarewaju, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aike wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata, a Ile-Ife.

Ya ce matakin na daga cikin kudurin da jami’ar ta yi na kawar da duk wani nau’i na cin zarafi a makarantar.

Sanarwar ta bayyana cewa majalisar ce ta yanke hukuncin korar Dr Adebayo Mosobalaje na Sashen Harshen Turanci ne, a zaman ta na karshe a ranar Talata, 7 ga watan Satumban 2021.

Ya kuma kara tabbatar da cewa Kwamitin hadin gwiwa da na ladabtarwar Jamiár ne suka gudanar da binciken a kan Dr. Mosobalaje, inda hukumomin jamiár suka yi nazari da daukar matakin.

A cewar sanarwar “Saboda hakan ne, hukumar gudanarwar jami’ar ta kara bayyana rashin goyon bayan ta ga cin zarafin mata, ta kowace irin siga, inda ta dauki matakin da ya dace gameda irin wannan laifi kamar yadda yake cikin dokokin jami’ar.

“Kimanin makwanni biyu da suka gabata, mahukuntan Jami’ar sun kaddamar da dokokin yakar cin zarafin mata, inda matar gwamnan Ekiti da Osun, Mrs. Bisi Fayemi da Alhaja Kafayat Oyetola suka gabatar da kasidu, yayin da tsohon Shugaban Jami’ar Tai Solarin University of Education, dake Ijagun, Farfesa Yemisi Obilade ya kasance babban bako mai jawabi.

Sanarwar ta kara da cewa, “A wurare da dama, Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya sake nanata kudirin sa na tabbatar da manufar sa na yaki da cin zarafin mata da sauran munanan dabi’u.”

Yanzu dai, hukumar gudanarwar jami’ar, karkashin shugabancin Owelle Oscar Udoji, ta kuma yi alkawarin goyon bayan manufofin inganta zaman tare da fahimta tsakanin membobin Jama’ar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here