JAMB ta fara tantance cibiyoyin CBT don jarabawar UTME ta 2025 

JAMB new

 

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Kasa (JAMB) ta fara aikin tantance Cibiyoyin Gwajin Na’ura (CBT) domin shirye-shiryen Jarabawar Shiga Jami’o’i ta 2025 (UTME).

Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, yana mai jaddada mahimmancin wannan tantancewa don tabbatar da gudanar da jarabawar cikin kwanciyar hankali.

Sanarwar ta bukaci sabbin cibiyoyin CBT da ke sha’awar shiga jarabawar UTME ta 2025 su duba sharuddan da aka gindaya a shafin intanet na JAMB.

Sabbin cibiyoyi za su iya ziyartar shafin JAMB don fahimtar ka’idojin tantancewa sannan su rubuta takardar sanarwa ga Shugaban Hukumar ta hannun Daraktan Yanki ko Ko’odinetan Jiha na su.

Ga cibiyoyin da aka tantance kuma suka gudanar da jarabawar UTME ta 2024 ba tare da wata matsala ba, an bukace su su nuna sha’awarsu ta hanyar Rajistar Cibiyoyin Gwaji a Manhajar CMS.

Sabbin cibiyoyin kuwa za su samu taimako daga ofisoshin JAMB na Jihohi da Yankuna wajen bude asusun su a CMS don fara rajista.

“Duk cibiyoyi dole ne su kammala gwajin na’ura mai suna Autobot/Autotest a ranar da za a sanar da su, a matsayin wani bangare na shirin tantancewar gani da hukumar za ta gudanar,” inji sanarwar.

Dakta Benjamin ya kara da cewa, cibiyoyin da suka kammala gwajin Autobot/Autotest cikin nasara tare da cika ka’idojin JAMB ne kadai za su ci gaba da mataki na gaba na tantancewar.

Za a fara aikin tantancewar gani a watan Disamba na 2024, inda cibiyoyin da suka cancanta ne kadai za su sami sanarwa.

JAMB ta jaddada cewa cibiyoyin da suka kasa cika ka’idoji yayin gwajin Autobot/Autotest ba za a tantance su ba, kuma ba za a hada su a rajistar UTME ta 2025 da jarabawar ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here