Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana nasarar hallaka wasu gaggan ƴan bindiga a yayin hare-haren sama da aka kai a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe, Jihar Zamfara, a ranar 15 ga Nuwamba.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na NAF, Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa aikin da ake gudanarwa a ƙarƙashin shirin Operation Fansan Yamma ya nufi kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a wannan yanki.
Hare-haren da aka yi, wanda suke ƙarƙashin shirin Farautar Mujiya, sun mayar da hankali kan rushe ƙungiyoyin ƴan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Akinboyewa ya ce rahotannin sirri sun nuna cewa ƴan bindigar suna shirye-shiryen kai hare-hare masu tsari kan jami’an tsaro da farar hula a hanyar Tsafe.
Bisa wannan bayanan, NAF ta aiwatar da hare-haren sama masu tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar shugabannin ƙungiyoyin ƴan bindiga da dama, ciki har da waɗanda suke biyayya ga shugabanni kamar Dan-Isuhu da Dogo Sule.
“Rahotanni daga ƙasa sun tabbatar da cewa an samu nasarar kashe yawancin manyan shugabannin waɗannan ƙungiyoyi, wanda hakan ya dakile aikinsu matuƙa,” in ji shi.
Ƙaramar Hukumar Tsafe ta dade tana zama cibiyar ayyukan ƴan bindiga, inda ake amfani da ƙauyukan da suka haɗa da Babban Kauye a matsayin mafaka don shirya hare-haren su.
Wadannan hare-haren sama na baya-bayan nan suna cikin matakan da ake ɗauka don kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da dawo da zaman lafiya a yankin.
Air Commodore Akinboyewa ya tabbatar da aniyar NAF na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da barazanar ƴan bindiga, ‘yan ta’adda da duk wasu ɓatagari a faɗin ƙasa.
Rundunar sojin saman na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.