Ka guje fadan kalaman da zasu kai ga raba kan yan Najeriya – Ata ga Kwankwaso

Abdullahi Ata

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa a 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya guji furta kalaman da ka iya kara raba kan yan Najeriya.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa Sanata Rabiu Kwankwaso wanda ya taba zama gwamna har sau biyu kuma tsohon minista, ya yi zargin cewa Legas na yunkurin mamaye Kano ne ta hanyar yin katsalandan a zaben da aka yi na zaben Sarkin jihar ranar Lahadi a taron jami’ar Skyline.
Ata ya jaddada cewa kalaman Kwankwaso suna da nauyi sosai kuma suna iya haifar da sakamako mai nisa, wanda zai iya zafafa harkokin siyasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here