Gwamnatin tarayya ta kammala horas da masu gadin dazuka sama da 7,000, don tura su aikin yaƙar matsalar tsaro

WhatsApp Image 2025 12 27 at 18.29.28 1 750x536 1 750x430 (1)

Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ta sanar da kammala horas da sababbin masu gadin dazuka sama da 7,000 da aka ɗauko daga jihohi bakwai, bayan sun kammala horo na tsawon watanni uku a ƙarƙashin shirin masu gadin dazuka na shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya ƙaddamar a watan Mayu 2025.

Shirin tsaro ne na haɗin gwiwar tarayya da jihohi da aka tsara domin kwato dazuzzukan Najeriya daga hannun masu aikata laifuka, tare da dakile amfani da su a matsayin mafaka da wuraren aikata ayyukan ta’addanci da sauran miyagun laifuka.

An gudanar da bukukuwan kammala horon a jihohin Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi, inda aka bayyana cewa shirin zai ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida ta hanyar hana ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane samun mafaka a yankunan dazuzzuka da wuraren da ke da wahalar isa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa horon ya kasance mai tsauri da tsari, inda aka mayar da hankali wajen sauya matasa masu kishin ƙasa zuwa jajirtattun jami’an aiki masu bin doka da oda, tare da haɗa darussan kiyaye muhalli da ƙwarewar tsaro ta zamani domin samar da runduna mai kwarewa da shirye-shirye.

Masu horaswar sun sha gwaje-gwajen jiki da na tunani, ciki har da atisayen juriya, ketare shinge da kwaikwayon sintiri na dogon lokaci, tare da koyon dabarun filin aiki kamar motsi, tinkarar abokan gaba, kare kai daga kwanton bauna, aikin ceto da kai hare-hare cikin tsari, domin hana masu laifi samun kowace irin mafaka a dazuzzukan ƙasa.

Haka kuma, an ba da muhimmanci ga ɗabi’a, bin doka da ƙwarewa, inda aka mayar da hankali kan haƙƙin ɗan Adam, dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, haƙƙin jinsi da kare fararen hula, tare da tsauraran ka’idoji kan sarrafa makamai da amfani da ƙarfi bisa littafin kula da makamai da hukumomin da suka halarta suka amince da shi.

Gwamnatin ta bayyana cewa tura masu gadin dazuzzukan aiki zai fara nan take ba tare da jinkiri ba, albashi da alawus-alawus za su fara aiki kai tsaye, yayin da aka tabbatar da cewa mafi yawan mahalarta sun kammala horon cikin nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here