Jimillar kuɗaɗe Naira Tiriliyan 1.928 aka raba na kwamitin rabon arzikin ƙasa na tarayya FAAC a watan Nuwamba tsakanin gwamnatın tarayya, jihohi da kuma ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
Kwamitin ya bayyana cewa an raba kuɗin ne a taron kwamitin na watan Nuwamba da aka gudanar a Abuja, inda aka amince da rabon kuɗaɗen shiga na watan.
Jimillar Naira Tiriliyan 1.928 ɗin ta ƙunshi kuɗaɗen haraji na doka wanda za a raba Naira Tiriliyan 1.403, sai kuɗaɗen harajin kaya da ayyuka Naira Biliyan 485.838, da kuma kuɗaɗen haraji na lantarki Naira Biliyan 39.646.
Sanarwar kwamitin ta nuna cewa jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya na watan sun kai Naira Tiriliyan 2.343, inda aka cire Naira Biliyan 84.251 a matsayin kuɗin tattara haraji, sannan aka ware Naira Biliyan 330.625 don canje-canje, tsoma baki, mayar da kuɗi da tanadi.
Rahoton ya ƙara da cewa an samu kuɗaɗen shiga na doka na da suka kai Naira Tiriliyan 1.736 a watan Nuwamba, adadin da ya ragu da Naira Biliyan 427.969 idan aka kwatanta da Naira Tiriliyan 2.164 da aka samu a watan Oktoba.
Haka kuma, an samu kuɗaɗen shiga na Naira Biliyan 563.042 daga harajin ƙima na kaya da ayyuka, wanda shima ya ragu da Naira Biliyan 156.785 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Daga cikin jimillar Naira Tiriliyan 1.928 da aka raba, gwamnatın tarayya ta karɓi Naira Biliyan 747.159, yayin da gwamnatocin jihohi suka karɓi Naira Biliyan 601.731, yayin da ƙananan hukumomi suka samu Naira Biliyan 445.266.
Haka kuma, an raba Naira Biliyan 134.355, wanda kashi 13 ne na kuɗaɗen ma’adinai, ga jihohin da suka amfana a matsayin kuɗin rabon hakar albarkatu.
A kan kuɗaɗen shiga na doka na Naira Tiriliyan 1.403, gwamnatın tarayya ta karɓi Naira Biliyan 668.336, jihohi suka samu Naira Biliyan 338.989, sai ƙananan hukumomi kuma suka karɓi Naira Biliyan 261.346.
Daga kuɗaɗen harajin ƙima na kaya da ayyuka na Naira Biliyan 485.838, sai gwamnatın tarayya ta samu Naira Biliyan 72.876, yayin da jihohi suka karɓi Naira Biliyan 242.919, sai kuma ƙananan hukumomi kuma suka samu Naira Biliyan 170.043.
Daga kuɗaɗen haraji na lantarki da ya kai Naira Biliyan 39.646, gwamnatın tarayya ta samu Naira Biliyan 5.947, sai jihohi suka karɓi Naira Biliyan 19.823, yayin da ƙananan hukumomi kuma suka samu Naira Biliyan 13.876.













































