kotun tarayya ta saka rana don gudanar da taron shekara-shekara na alkalan kotu

federal high court abuja

Kotun tarayya dake Abuja ta sanar da cewa za ta fara taron shekara-shekara na alkalan kotu a ranar 15 ga watan Disamba domin kaddamar da sabuwar shekarar shari’a ta 2025/2026.

Daraktar yada labarai ta kotun, Dakta Catherine Christopher, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a Abuja, inda ta ce babban alkalin kotun, Mai Shari’a John Tsoho, ya bayyana cewa taron zai ƙare a ranar 18 ga watan Disamba.

Sanarwar ta bayyana cewa taron shekara-shekara na alkalan kotun yana zama dandalin tunani da kimantawa da kuma tsara dabaru domin inganta gudanar da shari’a da haɓaka ingancin aikinta.

Haka kuma, taron yana nuna bude sabuwar shekarar shari’a ta kotun tarayya tare da fitar da cikakken bayani game da lokacin hutun kotun a nan gaba.

Babban alkalin kotun, Mai Shari’a John Tsoho, ya aika da fatan alheri ga dukkan alkalan da za su halarci taron tare da yi musu fatan samun sabuwar shekara mai cike da nasara.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here