A ranar Larabar da ta gabata ne gidajen sayar da man fetur na NNPC da kuma gidajen mai masu zaman kansu suka fara siyar da man fetur da ya kai Naira 1,065 a kowace lita a Abuja, da kuma N998 a Legas a cikin sabbin farashinsa a fadin jihohin Najeriya.
Kafin haka dai, jaridar Premium Times ta bayyana cewa, kamfanin na NNPC ya yi watsi da yarjejeniyar samar da kayayyaki na musamman da Dangote, wanda hakan ya ba ‘yan kasuwa damar tattaunawa kan farashi kai tsaye da matatar.
Farashin da aka ambata ya kasance tsakanin N1,030 zuwa N1,065 kowace lita a Abuja, N998 kowace lita a tashoshin NNPC da ke Legas, N1,025 a sauran jihohin Kudu maso Yamma, tsakanin N1,060 zuwa N1,070 a jihohin arewa maso gabas, da kuma tsakanin N1. ,055 da kuma N1,075 jihohin kudu maso kudu
Tun lokacin da matatar man Dangote ta fara aiki a watan Mayu, dangantakarta da NNPC ta yi tsami. A cewar Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, NNPCPL ta yi asarar kashi 20% na hannun jarin matatar bayan ta gaza biyan bukatun kudi.