A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, NCAA, ta dakatar da wani jirgin saman Rano mai lamba 5N-BZY, wanda ya samu matsala a injinsa mai lamba 1.
Sai dai lamarin ya haifar da cikas ga zirga-zirgar fasinja, musamman ma matafiya da ke shirin tashi daga Sakkwato zuwa wasu wurare.
Hukumar ta NCAA ta bayyana cewa an gano hayaki a cikin dakin jirgin da abin ya shafa, lamarin da ya sa aka fara aiwatar da hanyoyin gaggawar da suka dace domin tsairatar da fasinjojin.













































