Shettima ya dawo Najeriya bayan taron Kungiyar Tarayyar Afirka

Shettima Returns 750x430

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan halartar Babban Taron Shugabannin Kasashe da Gwamnatocin Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) na 21 da aka yi a birnin Luanda na kasar Angola.

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne a babban taron, inda Najeriya ta yi kira da a samar da kwakkwaran tsari karkashin jagorancin Afirka don yin riga-kafi da magance rikice-rikice, ta kuma bukaci adaukar matakin gaggawa a fadin nahiyar kan hare-haren kyamar baki da ke ci gaba da faruwa kan ‘yan Afirka da sauran ‘yan kasashen waje a kasar Afirka ta Kudu.

A wurin taron, Najeriya ta kuma marawa Shirin Aikin Luanda baya, inda ta yi kiran da a samar da kudad domin tsarin tsaro da zaman lafiya na Afirka da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta AU, da kuma nuna kishin Afirka wajen samar da mafita ga rikice-rikicen nahiyar.

Mataimakin Shugaban Kasar ya dawo Birnin Tarayya Abuja bayan kammala ayyukansa a kasar Angola.

Rashin shi a kasar ya haifar da damuwa, inda masu kushe gwamnati suka soki tafiyar Shugaba Tinubu zuwa Turai na tsawon makonni uku domin hutu, a daidai lokacin da mataimakinsa ke kasar waje.

Hakeem Baba-Ahmed, Shugaban Jam’iyyar PRP na Kasa, ya tayar da batun a taron G100 da aka yi a Abuja a farko a ranar Litinin.

“Muna da shugaban kasa da ke wajen kasa, yana kokarin boyewa ‘yan Najeriya gaskiyar abin da ka iya faruwa shekaru da dama da suka gabata lokacin da yake Amurka dangane da miyagun kwayoyi,” in ji shi.
“Mataimakinsa kuma yana Angola. Watakila wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar nan da kake da shugaban kasa a wajen kasa, kuma mataimakin shugaban kasa ma yana wajen kasa.”

Daga bisani, shugaban na PRP ya tambayi inda shugabancin Najeriya yake, yana mai cewa, “Wane ne ke jan ragamar kasar yanzu?”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here