Tinubu ya bukaci Tarayyar Afirka (AU) ta dauki mataki kan hare-haren kyamar baki a Afirka ta Kudu

Kashim Shettima AU

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake yin Allah wadai da hare-haren kyamar baki da na nuna adawa da ‘yan Afirka da ke faruwa akai-akai kan ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen Afirka a Afirka ta Kudu, ya bukaci shugabannin Afirka da su dauki matakin gaggawa na bai-daya domin kawo karshen tashe-tashen hankula tare da kare mutuncin ‘yan kasa a duk fadin nahiyar.

Haka kuma, Tinubu ya bukaci Tarayyar Afirka (AU) da ta tattauna kan batun a hukumance a babban taronta na gaba, inda ya gargadin cewa hare-haren da ake kai wa ‘yan uwa ‘yan Afirka na gurgunta manufofin hadin kai, daidaito da zaman lafiyar nahiyar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya isar da sakon Shugaban Kasar a ranar Lahadi yayin Babban Taro na Musamman karo na 21 na Shugabannin Kasashe da na Gwamnatocin AU da aka gudanar a Luanda na kasar Angola.

Wannan mataki ya nuna yadda Najeriya ta tsananta yunkurinta na diflomasiyya domin samun goyon baya daga daukacin nahiyar kan kiyayyar da ake nunawa bakin haure ‘yan Afirka a Afirka ta Kudu.

Wannan na zuwa ne makonni shida kacal bayan da Tinubu ya gabatar da batun a gaban shugabannin Yammacin Afirka, inda ya bukaci su hada kai wajen yakar hare-haren.

“Najeriya na son bayyana damuwarta kan hare-haren kyamar baki da na nuna adawa ga ‘yan Afirka da ke faruwa akai-akai kan ‘yan Afirka da sauran ‘yan kasa a Afirka ta Kudu,” in ji Shugaban Kasar a sakon da Shettima ya isar.

Yayin da yake amincewa da ikon Pretoria na tsara dokokin shige da fice da tabbatar da dokokinta, Tinubu ya jaddada cewa aiwatar da dokokin shige da fice ba zai zama dalilin yin amfani da karfi ko kai wa ‘yan kasashen Afirka hari ba.
“Yayin da muke mutunta ikon Afirka ta Kudu na aiwatar da dokokin shige da fice da kuma amincewa da gudunmawar da take bayarwa ga nahiyar, Najeriya na jaddada cewa irin wadannan hare-hare suna gurgunta hadin kan Afirka da zaman lafiya, kuma suna bukatar daukar matakin gaggawa na bai-daya,” in ji shi.

Shugaban Kasar ya bukaci Majalisar AU da ta sake jaddada alhakin da ke kanta na tabbatar da tsaro da mutuncin ‘yan Afirka a duk inda suke zaune.

“A wannan gaba ne Najeriya ke kiran wannan babban taro da ya sake jaddada kudorinsa na tabbatar da tsaro, kariya da mutuncin dukkan ‘yan kasashen Afirka. Ya kamata a karfafa gwiwa wajen yakar kyamar baki, sannan a sanya batun a cikin jadawalin Babban Taro karo na 40 na AU da za a yi a watan Janairun 2027 domin duba shi da daukar matakin da ya dace,” in ji shi.

Wannan sabon yunkuri na Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da aka sake samun bullar fafutuka da hare-haren adawa da bakin haure a Afirka ta Kudu a wannan shekarar, inda ‘yan Najeriya da ‘yan wasu kasashen Afirka da dama suka fuskanci barazana, tursasawa da tashe-tashen hankula.

Ana danganta wannan rikici da kamfen din adawa da baki da wasu kungiyoyi ke yi, wadanda ke zargin baki ‘yan Afirka da janyo rashin aikin yi, aikata laifuka da sanya matsin lamba ga ayyukan jin dadin jama’a a Afirka ta Kudu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ruwaito a watan Mayu cewa, sabon salon fafutukar adawa da bakin hauren ya shafi kungiyoyin sa-kai na sa-ido, ciki har da ‘Operation Dudula’ da ‘March and March’, a wasu lokutan ma ana hana baki damar samun ayyukan lafiya da na ilimi na gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here