Hukumar DSS ta dakatar da shari’ar Sowore har sai bayan zaben shugaban kasa na 2027

Sowore 2

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde (SAN), da ya nemi a dage shari’ar da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, kan zargin laifin yanar gizo har sai bayan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

A cewar wata majiya mai tushe, an dauki wannan matakin ne domin ba wa Sowore damar shiga cikin harkokin yakin neman zabe gadan-gadan ba tare da gudanar da shari’ar ya zame masa cikas ga ayyukansa na siyasa ba.

Hukumar DSS ta shigar da kara kan Sowore ne saboda wasu rubuce-rubuce da ya yi a kafafen sada zumunta inda ya kira Shugaba Bola Tinubu da “mai laifi”.

Wadannan rubuce-rubuce, wadanda aka wallafa a shafin X na Sowore da kuma shafinsa na Facebook a ranar 25 ga Agusta, 2025, sun sa ‘yan sandan asiri suka ba shi wa’adin kwanaki bakwai da ya goge su.

Bayan cikar wa’adin ba tare da an goge rubuce-rubucen ba, DSS ta garzaya gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar 16 ga Satumba, 2025, inda take neman fassarar shari’a kan ko ya halatta mutum ya fito fili ya kira Shugaban Kasa ko wani mutum daban da “mai laifi”.

Da fari, hukumar ta sanya kamfanin X da kuma Meta (mamallakin Facebook) a cikin karar, sai dai daga baya, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta cire kamfanonin fasahar guda biyu daga shari’ar, inda ta bar Sowore shi kadai a matsayin wanda ake kara.

Sowore ya bayyana cewa ba shi da laifi a kan sabbin zargin da aka yi masa a karkashin Dokar Laifukan Yanar Gizo ta shekarar 2024 (Cybercrimes Act 2024).

Ya sha sukar wannan shari’a, inda yake bayyana ta a matsayin wata kullalliyar siyasa da ke neman takaita masa ‘yancin fadin albarkacin baki.

Shi ma mai fafutukar ya shigar da kararrakin kare hakkin bil’adama da hukumar DSS da kamfanonin fasahar, inda yake kalubalantar abin da ya kira kokarin tursasa masa.

Sai dai wata majiya ta kusa da tawagar lauyoyin DSS ta ce Darakta Janar na hukumar, Tosin Ajayi, ya gana da babban lauyan da manyan jami’an sashen shari’a na hukumar a ranar 20 ga Agusta domin nazarin dakatar da shari’ar.

A cewar majiyar, taron ya zo ne jim kadan bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage takunkumin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027.

Majiyar ta ce: “Shugaban na DSS ya shaida wa Babban Lauyan da sashensa na shari’a cewa, da yake an fara yakin neman zaben shugaban kasa, zai kasance adalci a dakatar da shari’ar kotun domin bai wa Sowore damar shiga cikin zabuka masu zuwa ba tare da wata tsangwama ba.”

Majiyar ta kara da cewa Ajayi ya shaidawa lauyoyin cewa lamarin ya riga ya kwashe kusan shekara guda a kotu, saboda haka dakatar da shi na wasu watanni hudu ba zai haifar da wani babban bambanci ba.

Haka zalika, an ce DSS ta umarci tawagar lauyoyinta da su duba makamantan wadannan shari’o’i da suka shafi ‘yan takara masu neman wasu mukaman na zabe.

Hukumar a baya ta jaddada cewa shari’ar Sowore na nufin samun fassarar shari’a ne kawai kan dacewar kiran Shugaba Tinubu ko wani mutum da “mai laifi”, maimakon kawai a takaita ayyukan siyasar Sowore.

A cikin wata wasika ranar 6 ga Satumba, 2025 zuwa ga shugaban kamfanin Meta, DSS ta ce babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare Shugaban Kasa ya wuce barazanar zahiri, har da hare-haren da ke taba kima da daraja.

Majiyar ta ce ana sa ran isar da matakin DSS na dakatar da shari’ar a hukumance ga Babbar Kotun Tarayya daga ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026, lokacin da kotun za ta ci gaba da zama na yau da kullum bayan hutu shekara-shekara.

Sowore, wanda a baya Babbar Kotun Tarayya ta ba shi belin kansa, ana sa ran zai ci gaba da harkokinsa na siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here