Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da har zuwa yan zu ba’a ganshi a gidan gyaran halin ba, tun bayan halirn da ‘yan bindiga suka kai gidan da ya dauki tsawon sa’o’i kadan, an ce jami’an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.
Wani jami’i wanda baya su a bayyana sunan sa, ya ce har yan zu bai san inda Kyari yake ba.
“na tabbatar bai gudu ba, amma ban san inda yake ba a yanzu haka”
Yayin da ake tambayar kakin hukumar, Umar Abubakar ya ce Kyari bai bata ba.
“Har yanzu yana hannun mu, ba kuma abin da ya faru dashi”













































