An nada sabon sakataren din-din-din a ma’aikatar albarkatun Man fetir ta kasa

nigeria federal ministry for petroleum resources logo 1
nigeria federal ministry for petroleum resources logo 1

An nada Gabriel Aduda a matsayin sabon babban Sakatare a ma’aikatar albarkatun Man Fetur.

Cikin wata sanarwa da babbar Daraktan yada labarai uwargida Enefaa Bob–Manuel ta sanyawa hannu, ta ce an tura Aduda ne bisa amincewar shugabancin Ma’aikatar.

Da yake jawabi yayin liyafar maraba da Daraktocin Ma’aikatar, Aduda ya bukace su da su ajiye banbance-banbance da ra’ayoyinsu na daidaikunsu, su yi kokarin ciyar da ma’aikatar da kasa gaba.

Sakataren na din din din ya bayyana shirin yin aiki tukuru domin ganin ma’aikatar ta samu nasarar aikin ta a bangaren mai da iskar gas.

Aduda ya yi kira da a samar da ingantattun hanyoyi da hanyoyin hulda da hukumomi daban-daban a bangaren da nufin bunkasa masana’antar mai da iskar gas ta duniya.

Babban Sakatare daganan ya godewa magabata bisa wannan kyakkyawan aiki da suka fara da ya kawo su zuwa wannan mataki.

Ya yaba wa Daraktocin bisa yi masa kyakkyawar tarba tare da ba da tabbacin cewa zai yi amfani da manufofi masu dama don ba su damar hulda da shi cikin walwala.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here