ASUU ta jami’ar jihar Filato ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani

C80B707A ED97 4D09 B8E9 30C79103A272
C80B707A ED97 4D09 B8E9 30C79103A272

Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU reshen jami’ar Jihar Filato, ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Litinin don matsawa bukatunta na inganta walwala da muhallin aiki.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Jos tare da sanya hannun Dakta Hassan Zitta da Deme Bitrus, shugaba da sakatare na kungiyar.

Kungiyar ta ce an cimma matsayar ayyana yajin aikin ne a zaman da kungiyar ta  gudanar a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa gwamnatin Filato ta gaza mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar, don haka ta yanke shawarar daukar matakin da ya dace.

Kungiyar a cikin sanarwar ta kuma bayyana cewa, matsalar da ake fama da ita tana da nasaba da karuwar rashin tsaro a jami’ar da kuma rashin biyan kudaden alawus-alawus.

Dalilan, kungiyar ta ce akwai karancin wurin kwana ga dalibai da ma’aikata da kuma bukatar gwamnati ta gina karin dakunan karatu da dai sauransu.

Sanarwar ta ce majalisar ta yanke shawarar cewa gwamnatin jihar bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar a ranar 2 ga Maris, 2021 ba ta amince da takardar ba.

ASUU ta ce gwamnatin Filato ta kuma kasa gina ofishin ‘yan sanda a cikin jami’ar da kuma gazawarta wajen biyan bashin mafi karancin albashi na kasa a cikin kwata na farko na shekarar 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here