Kungiyar malaman jami’o’i ASUU, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyar da suka ƙulla ta shekerar 2009 ko kuma ta su tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar ta ASUU Chris Piwuna, ne ya yi wannan gargadin yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Ya jaddada mahimmancin gwamnati ta cika alkawuran da ta dauka da kuma magance tabarbarewar yanayi a jami’o’in Najeriya.
A cewar Piwuna, har yanzu ba a warware wasu muhimman batutuwa guda tara ba, ciki har da tsarin sake tattaunawa da ya tsaya cik tun daga shekarar 2017.
Haka kuma ya ambaci hana albashi daga yajin aikin 2022 da kuma rashin biyan haƙƙoƙin da ke da alaƙa da rikice-rikicen sabon tsarin biyan albashi na IPPIS.
Piwuna ya kuma soki jinkirin fitar da kudaden farfado da harkar ilimi da kuma samun alawus alawus na ilimi saboda gazawar gwamnati. Duk da alkawuran da aka yi na zuba Naira biliyan 150 a jami’o’i tare da daidaita alawus-alawus na yau da kullum nan da shekarar 2026, ya ce wadannan alkawurra sun ci gaba da kasancewa ba a cika su ba.
Ya bayyana yadda ake mayar da ‘ya’yan kungiyar ASUU saniyar ware a cibiyoyin gwamnati kamar Jami’ar Jihar Kogi da Jami’ar Jihar Legas.
A cewarsa cin zarafi da rashin albashi da kuma rashin aikin yi na ci gaba da tabarbarewa a wadannan jami’o’in, wanda hakan ke kawo wa ma’aikata kwarin gwiwa.
Dangane da ‘yancin cin gashin kan jami’o’in, ya ce tsoma bakin siyasa ya kawo cikas ga zaben shugabannin, inda ya bayar da misali da Nnamdi Azikiwe da jami’o’in Abuja.
Piwuna, ya yi gargadin cewa jami’o’i na zama fagen fama na siyasa da tattalin arziki, abin da ya bayyana a matsayin wanda ba za a amince da shi ba.
Haka kuma, Don magance rikicin, ya ba da shawarar taron koli na ilimi na kasa wanda ke mai da hankali kan kudade, cin gashin kai, da walwalar ilimi.













































