Gwamnatin tarayya ta umarci shugabanin jami’o’in Najeriya dasu bude makarantun su

ASUU strike
ASUU strike

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta bawa shugabanin jami’o’in Najeriya umarni da su bude makarantu don bawa dalibai dama su cigaba da karatu ba tare da bata lokaci ba.

Bayanin hakan na cikin takardar da gwamnatin tarayya ta rabawa manema labarai ranar Litinin, wacce akanta na hukumar NUC, Sam Onazi, ya sawa hannu a madadin sakataran hukumar ta NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ya umarci shugabanin jami’o’in dasu bude makarantun su ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar ta ASUU dai ta shafe sama da watanni bakawai tana gudanar da yajin aiki domin tlisatawa gwamnatin tarayya ta biyawa mata bukatun ta.

Sasanci ya gagara tsakanin kungiyar da gwamnatin inda har ta kai ga gwamnatin tarayya ta maka kungiyar ASUU a kotu domin tilasta mata dawo bakin aiki.

A satin da ya gabata kotun ma’aikata karkashin mai shara’a Polycarp Hamman, ta bawa ASUU umarnin dawowa bakin aiki ba tare da bata lokaci ba,
Biyo bayan umarnin na kotun, kongiyar ta dauki matakin daukaka kara domin kalubalantar hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here