Mutane 2 sun jikkata yayin da jirgin da suke ciki ya yi hatsari a Ilorin

Two injured as training aircraft crash lands

Hukumar bincike kan hadurra da tabbatar da tsaro ta Najeriya NSIB, ta bayyana cewa wasu mutane biyu da ke cikin wani jirgin horas da direbobi na Diamond da ke makarantar horaswar jiragen sama da ke Ilorin, sun samu raunuka kuma an kwantar da su a asibiti bayan rikitowar da jirgin da suke ciki ya yi.

Hukumar NSIB ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan wannan matsala kamar yadda wata sanarwa da ta fitar a daren ranar wadda Daraktar hulda da Jama’a ta Ofishin hukumar Misis Bimbo Oladeji, Inda ta ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:28 na yammacin a ranar 23 ga watannan da muke ciki na Mayu.

Ta kuma bayyana cewa jirgin ya kauce daga titinsa ne inda ya tsaya a cikin ciyawa.

Haka Kuma a cewar sanarwar, “Mutane biyu ne a cikin jirgin, kuma dukkansu sun samu munanan raunuka, kuma an dauke su cikin gaggawa zuwa wani asibiti, wanda hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NAMA ta tsara.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here