Wata kotun tarayya a Amurka ta dakatar da wata doka da Ma’aikatar Tsaron Ƙasa (Department of Homeland Security) ta fitar, wadda ke hana Jami’ar Harvard ɗaukar ɗaliban ƙasashen waje.
Alkalin Kotun Ƙasa, Jeffrey White, ne ya dakatar da wannan doka bayan Kristi Noem, Sakatariyar Ma’aikatar Tsaron Ƙasa, ta bayyana dokar a hukumance ranar Alhamis.
Alkali White ya kuma hana gwamnatin Amurka kama, daure ko mayar da ɗaliban ƙasashen waje zuwa wasu wurare har sai an yanke hukunci a karar da ke kalubalantar soke sahihancin zama na wasu daga cikinsu.
A tsakanin watan Maris da Afrilu, sama da ɗalibai 4,700 daga ƙasashen waje aka soke musu izinin karatu a Amurka ba tare da gargaɗi ba.
Wani yanki na ɗalibai kusan 24 ne suka shigar da ƙara a kotu domin kalubalantar wannan mataki.













































