Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahir M. Hashim, ya samu lambar yabo ta ISTF Green Award a taron kasa na 2025 da kungiyar International Society of Tropical Foresters (ISTF) ta shirya a Kano.
Lamarin ya nuna yabo ga kokarinsa da na gwamnatin jihar wajen inganta muhalli da kyakkyawan shugabanci.
A jawabinsa, Dr. Hashim ya bayyana cewa nasarar na da alaka da hadin gwiwar jama’a da masu ruwa da tsaki a fannin kare muhalli a Kano.
Ya kuma sanar da sabbin tsare-tsare, ciki har da kara albashi da daukar sabbin masu gadin daji, shirin dasa itatuwa a fadin jihar a 2025, da matakai na rage gurbacewar muhalli da farfado da dazuka.
Ya bukaci al’umma su taimaka wajen kare muhalli ta hanyar hana sare itatuwa ba bisa ka’ida ba da wayar da kai a cikin al’umma.













































