Jami’ar KHAIRUN ta taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 69 a duniya 

RMK RMK 554x430

Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano (KHAIRUN) ta mika fatan alheri ga tsohon Sanata na jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da yake cika shekaru 69.

A cikin wata sanarwa da Ag. Daraktan harkokin jami’ar da Tallace-tallace, Bilal Dahiru Tijjani, ya sanya hannu a ranar Talata, ta ce shugaban Jami’ar Farfesa Abdulrashid Garba, a madadin majalisar zartarwa, ma’aikata, da dalibai sun bayyana sanata Kwankwaso a matsayin jagora mai hangen nesa, dan kasa mai kishin kasa, mai himma wajen ilimi.

Farfesa Garba ya yaba da jajircewar tsohon gwamnan wajen bunkasa hazikan mutane, inda ya nuna cewa ayyukansa na ci gaba da zama abin koyi ga zamani a Najeriya da ma kasashen waje.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Sanarwar ta jaddada cewa gudummawar Sanata Kwankwaso a fannin ci gaban ilimi, inganta ababen more rayuwa, da karfafa matasa sun zama tarihi na jagoranci mai ma’ana da hidima ga al’umma.

Farfesa Garba ya kuma yi addu’a domin ci gaba da samun lafiya, hikima, da karfin jiki ga Sanata Kwankwaso, tare da nuna amincewa cewa kaunar sa ga ci gaban kasa za ta ci gaba da kawo tasiri mai kyau ga Najeriya.

Dukkanin al’ummar KHAIRUN sun taya murnar wannan rana, suna yi masa fatan samun karin shekaru masu albarka na hidima ga kasa da al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here