Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwarsa da za ta kasance a ranar 21 ga Oktoba, 2025, inda ya bayyana cewa har yanzu yana ɗaya daga cikin abokansa na kusa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ƙasa ya mika sakon taya murna ga iyalan Kwankwaso, abokai da abokan siyasa na kusa da shi yayin bikin ranar haihuwar tasa.
Tinubu ya yabawa Kwankwaso bisa irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wa Najeriya a matsayinsa na jagora a lokuta daban-daban.
Ya tunatar da rawar da Kwankwaso ya taka a matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai a lokacin mulkin jamhuriya ta uku da ta rushe, sannan a matsayin gwamnan jihar Kano har sau biyu, ministan tsaro, da kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa a jamhuriya ta huɗu.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa waɗannan mukamai sun bai wa Kwankwaso dama wajen bayar da muhimmiyar gudunmawa ga cigaban ƙasa.
Haka kuma, ya ce tasirin sa a siyasar arewa, musamman a jihar Kano, ya nuna cewa yana bin tsarin siyasa mai kishin jama’a, irin wanda marigayi Malam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi suka kafa.
Tinubu ya bayyana cewa Kwankwaso aboki ne kuma abokin aiki, wanda suka yi aiki tare tun daga majalisar dokoki ta shekarar 1992 da kuma lokacin da duka suka kasance gwamnoni a 1999.
Ya ƙara da cewa sun haɗa kai wajen kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin daga bisani Kwankwaso ya bar jam’iyyar ya kafa Jam’iyyar (NNPP), amma har yanzu yana cikin jerin masu akidar cigaba.
Shugaban ƙasa ya yi masa fatan alheri, lafiya da ƙarin shekaru masu albarka don ci gaba da bayar da gudunmawa ga cigaban Najeriya.













































