Majalisar zartawa ta kungiyar lauyoyi ta kasa NBA, ta dakatar da babbar sakatariyar ta, Joyce Oduah, daga ofishin ta.
A yau Litinin, kungiyar ta ce ta dakatar da ita ne bisa rashin bin dokokin kungiyar, hakan ya sa NBA ta kira taron majalisar zartawa ta kungiyar a ranar 21 ga watan Agusta na shekarar 2022, domin hukun tata.
Ya yin zaman na majalisar zartawarsa, ta cimma matsaya akan dakatar da ita daga ofishin ta domin gudun karta jefa kungiyar cikin halin da bazata iya fita ba.










































