Gwamnatin Nijeriya ta dage takunkumin fitar da itace da gawayi zuwa ƙasashen waje

326675175 722307815926581 6040383810739395801 n
326675175 722307815926581 6040383810739395801 n
Gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumin kan fitar da itace da gawayi zuwa ƙasashen waje amma da “sharadi”.
Mohammed Abdullahi, ministan muhalli ne ya bayyana haka a Abuja a jiya Alhamis bayan wani taron tuntuba da masu ruwa da tsaki a harkar katako da gandun daji su ke yi.
Ya ce saka takunkumin ya shafi da dama daga cikin ƴyan kasuwa, inda ya ce an dauki matakin ne domin baiwa kamfanoni da masu zaman kansu damar saka hannun jari a harkar noman daji.
Ministan ya yi gargadin cewa gwamnati za ta sanya tsauraran matakai don dakile ɓata dazuzzuka da kuma tabbatar da dorewar kula da gandun daji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here