Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ya yi mamakin irin yadda ’yan jam’iyyar ke karuwa a jihar Legas gabanin babban zaben 2023.
Atiku Abubakar, wanda ya isa jihar da sanyin safiyar ranar Talata domin gudanar da jerin shirye-shirye, ya yi jawabi ne a taron masu ruwa da tsaki da ‘yan jam’iyyar da shugabanni da ‘yan takarar mukamai daban-daban a zabe mai zuwa.
“Yanzu, a duk tsawon rayuwata ta siyasa, baya ga kasancewata daya daga cikin mutanen da suka kafa PDP, ban taba ganin jihar Legas ta cika da Yan jamiyya kamar haka ba.
“Wannan ya sa na yi imanin cewa a wannan lokacin, PDP za ta ci zabe a jihar Legas. Na yi imani za ku lashe jihar Legas a wannan karon,” in ji Atiku.
Abubakar, wanda ya yi alkawarin marawa jam’iyyar baya domin samun nasara a zaben 2023 a jihar, ya bukaci masu ruwa da tsakin jam’iyyar su kara zage damtse wajen ganin an cimma wannan nasara.
“Saboda haka, a shirye muke mu ba ku goyon baya a kowane mataki don ganin kun ci nasara a jihar Legas.
“Saboda haka, ina son ku kara himma, za mu ba ku hadin kai, za mu ba ku goyon baya, mu kuma ba ku kariya don ganin cewa a wannan karon, kun ci jihar Legas,” in ji shi.
Dan takarar na PDP, wanda ya lura cewa ba a fara yakin neman zabe ba, ya ce ya je jihar ne domin ya ga halin da al’amura ke ciki a jam’iyyar.
Ya ce: “Na zo na ga cewa PDP na nan a jihar Legas, kuma na ga abubuwa da kaina.
Ya kuma yabawa ‘ya’yan jam’iyyar bisa goyon bayansu da hakuri da juriya.
A nasa jawabin, Dakta Olajide Adediran (Jandor) dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas, ya ce al’ummar jihar ba su taba samun yakini irin haka ga Abubakar ba.
Adediran ya ce ‘yan jam’iyyar a jihar sun yi magana da kansu kuma sun yanke shawarar mayar da hankali kan Abubakar kawai a matsayin “wanda zasu zaba a 2023.”
“Mun yi magana da kanmu kuma mun yanke shawarar cewa, ba tare da la’akari da duk wani abu da ke faruwa a ko’ina ba, abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne jamiiyar PDP ta kai gacin zabe a Najeriya da jihar Legas.
“Mun gode muku, mun yarda da ku, kuma muna daraja ku.
Abin da muke so kuma muke fata shi ne Atiku Abubakar ya zama Shugaban Tarayyar Najeriya a 2023 kuma abin da muke da shi ke nan.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Abubakar ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da Sanata Dino Maleye da Cif Raymond Dokpesi da sauran jiga-jigan jam’iyyar da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin kasar daga jam’iyyar.
Mambobin kwamitin zartaswar jam’iyyar na jihar Legas karkashin Philip Aivoji sun halarci taron tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar a jihar.













































