Kakakin Majalisar Kwara ya zama dan takarar gwamna a APC

Yakubu Danladi Salihu 750x430

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Mista Yakubu Danladi Saliu, ya lashe zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar APC a jihar gabanin zaben 2027.

Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwanin, Sanata Musiliu Obanikoro, ne ya sanar da sakamakon a ranar Juma’a a Ilorin.

Obanikoro ya ce Danladi Saliu ya samu kuri’u 94,990 ya yin da ya doke sauran ‘yan takara tara a zaben.

A cewarsa, Amb. Abdulfatai Yahaya Seriki ya zo na biyu da kuri’u 41,700, yayin da Olufemi Sanni ya samu kur”u 5,519.
Dr Yahaya Oloriegbe ya samu kuri’u 3,920, yayin da Mohammed Bergore (SAN) ya samu kuri’u3,411.

Mohammed Bio ya samu kuri’u1,122, Dr Alabi Oluwatoyin ya samu kuri’u 1,099, yayin da Bashiru Bolarinwa ya samu kuri’u 22,118.
Prof. Abubakar Suleiman ya samu kuri’u 1,722, yayin da Prof. Wale Suleiman ya samu kuri’u 2,434.

Obanikoro ya ce zaben fidda gwani, wanda aka dage a baya saboda wasu dalilai, ya shaida yawan fitowar mambobin jam’iyya cikin lumana a fadin jihar.

“Duk da rashin jin dadin da aka samu jiya, mambobi sun fito a yau da yawa domin yin zaen cikin lumana.

“Wannan ya nuna hadin kai, juriya da karfin jam’iyyarmu mai albarka,” in ji Obanikoro.

Ya ce babu wanda ya yi rashin nasara a zaben, inda ya bayyana dukkan ‘yan takarar a matsayin mambobin iyali guda na siyasa.

“Da haka na tabbatar da cewa Mista Yakubu Danladi Saliu, bayan ya cika sharuddan APC kuma ya samu mafi yawan kuri’u, na ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji Obanikoro.

Shugaban APC na Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya yaba wa mambobi bisa dabi’a da yanayi mai kyau da suka nuna a lokacin gudanar da zaben.

Fagbemi ya bayyana nasar gudanar da zaben fidda gwani a matsayin shaida ga shirin jam’iyyar na babban zaben 2027. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here