Wike ya canja sunan cibiyar taron kasa da kasa ta Abuja zuwa sunan Tinubu

President Bola Tinubu Nyesom Wike and other government officials 750x430

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya canja sunan cibiyar taron kasa da kasa ta Abuja zuwa Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre.

Ministan ya kuma bayyana cewa an canja wa wasu dakunan da ke ginin sunan mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da shugaban majalisar Dattawa  Godswill Akpabio da kuma shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas da na alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun.

Wike ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar cibiyar yau Talata a Abuja.

“A yau, wannan cibiyar taron kasa da kasa ta Bola Ahmed Tinubu za ta iya gogayya da duk wata cibiyar taro ta kasa da kasa, kuma an yi haka, domin ita ma majalisar dokokin kasar ta tallafa mana, ina shaida muku cewa a baya, muna da zauruka guda biyu, dole ne mu tuna wadanda su ma suka goyi bayan babban birnin tarayya Abuja kuma majalisar kasa na daya daga cikin irin wannan bangaren na gwamnati.

“Don haka mun sanya wa zauren taro daya sunan Tajudeen Abbas Hall, mun sanya wa dakin taro na Godswill Akpabio, kuma Mataimakin Shugaban kasa, sannan suna alkalin alkalai CJN.

Wike ya kuma danganta kammala ginin cibiyar taron da aka gyara ga shugabancin shugaba Tinubu, inda ya ce, “A cikin watanni takwas shugaban kasa muka yi wannan aiki.

Kuma na yarda da cewa in ba da shugabancinka ba, da ba zai yiwu ba.

“Ministan ya kuma bayyana cewa, duk ma’aikatu ko hukumomin gwamnati da suke son yin amfani da Cibiyar Taron, za su biya kudi domin kama haya don kula da ita yadda ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here