Rundunar sojin saman Najeriya ta Operation Haɗin-Kai, ta ce ta hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata muhimman kayayyakinsu a yankin Tafkin Chadi.
Sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin saman Ehimen Ejodame, ya fitar ta ce, an kai harin ne ranar 9 ga watan nan da muke ciki na Yunin, bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da ayyukan ta’adda a wajen.
Rundunar ta ce, hakan wani bangare ne na ci gaba da yaki da ƴan ta’adda a yankin, inda sojojin suka ƙaddamar da farmakin sama a Bukar Meram, wani sansanin horo da ƴan ta’addan ke mafaka a ciki a jihar Borno.
Kayan da aka lalata sun haɗa da wuraren ajiye makamai da kuma sansanoni da bata garin suka kafa.
Haka kuma rundunar sojin saman ta ce, wannan hari wani ɓangare ne na matakan riga-kafin da take ɗauka don hana ‘yan ta’adda damar sake kafa sansanoni ko kai hari a yankunan da aka ƙwato.













































