Farashin kayan gwari ya sauka da kashi 50 cikin 100 yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar nan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Za’a gama zanga-zanga ne mai taken #EndBadGovernance inNigeria a ranar 10 ga watan Agusta, kamar yadda masu zanga-zangar suka shirya.
Manufar zanga-zangar shine jawo hankalin Gwamnatin Tarayya kan matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Wasu ‘yan kasuwa da masu saye a kasuwar abinci ta Ile-epo da ke unguwar Alimosho/Agege a jihar Legas sun tabbatar da faduwar farashin kayan gwari a wata tattaunawa da suka yi da NAN a ranar Juma’a a Legas.
NAN ta ruwaito cewa kasuwannin abinci na yankin sun kasan ce a rufe saboda zanga-zangar yunwa da ake yi a fadin kasar.
Wani mai sai da tumatur a kasuwar Ile-Epo da ke yankin Agege, Mista Rabiu Aliu, ya ce farashin kayan gwari da suka hada da tumatur da barkonon chili da sauransu sun sauka don rage asara sakamakon babu masu siya.
zanga-zangar ta haifar. “A yanzu ana sayar da kwandon tumatur mai nauyin kilogiram 50 a tsakanin N40,000 zuwa N50,000 sabanin N80,000 zuwa N100,000 makonni biyu da suka wuce. “Ana sayar da kwandon kilo 25 tsakanin N18,000 zuwa N19,000 sabanin N30,000 zuwa N40,000 makonni biyu da suka wuce. “Ba mu da wani zaɓi sai dai mu sayar da shi saboda ’yan kasuwa kaɗan ne ke da damar siyan kayayyakin. Ƙarfin sayayya ya yi ƙasa sosai a halin yanzu,” in ji Aliu.
Ita ma wata ‘yar kasuwa mai suna Misis Mukit Afolabi, ta ce farashin kayayyakin da gwari ya ragu a kasuwar sakamakon zanga-zangar yunwa.