Gwamnatin jihohin Katsina da Plateau sun bayar da umarnin rufe makarantu saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga da ke afkawa cibiyoyin ilimi a wasu yankuna na kasar.
Kwamishinan ilimi na jihar Katsina, Yusuf Jibia, ya sanar da rufe makarantu a ranar Juma’a yayin tattaunawa da manema labarai.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare dalibai da malamai yayin da hukumomin tsaro ke aiwatar da sabon tsari na tabbatar da tsaron makarantu a fadin jihar.
Ya bayyana cewa umarnin ya shafi daliban da ke rubuta jarabawa a halin yanzu, yana mai cewa kiyaye rayuka da dukiyoyi shi ne abu mafi muhimmanci ga gwamnati.
A cewar sa, wannan rufewa mataki ne na wucin-gadi da zai ci gaba har sai an kammala cikakken binciken tsaro a yankunan da aka gano suna cikin haɗari.
Labari mai alaƙa: Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta rufe Makarantu guda 41
Kwamishinan ya ce darussan makarantu za su koma yadda suke bayan an tantance matsalar tsaro tare da samar da kariya mai inganci, sannan ya bukaci iyaye, malamai da mazauna yankuna su bi umarnin a yayin da jami’ai ke ci gaba da bibiyar yanayin tsaro.
A jihar Plateau, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar SUBEB, Richard Jonah, ya bayyana umarnin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Jos.
Ya ce umarnin ya nuna gaggawar ɗaukar matakin kariya domin kiyaye rayuka da dukiyoyi a jihar.
Ya bayyana cewa makarantu na sakandare mallakar gwamnati za su rufe daga Asabar, 22 ga Nuwamba, yayin da makarantun firamare da na jeka ka dawo za su rufe daga Litinin, 24 ga Nuwamba.
Jami’in ya kara da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi da aka dauka domin dakile barazanar tsaro, tare da tabbatar wa al’umma cewa gwamnati na fifita kyakkyawan makomar yara masu karatu.
Ya gargadi hukumomin ilimi na kananan hukumomi, shugabannin makarantu da jagororin al’umma da su tabbatar da bin cikakken umarni tare da kasancewa cikin shiri.
Matakan jihohin biyu na zuwa ne bayan sace daliban makarantu a jihohin Kebbi da Niger, lamarin da ya kara tayar da hankula tsakanin iyaye da hukumomi a yankin Arewa maso Yamma.













































