Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Musulmi su fara duban jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijiriyya daga ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.
Idan an ga jinjirin, watan Ramadan zai fara ne a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026; idan ba a gani ba, zai fara a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026.
A cikin wata sanarwa da sakatare Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede ya fitar, ya nuna damuwa kan kalubalen da Musulmi ke fuskanta a Najeriya, inda ya ambaci karuwar kyamar Musulunci, matsalar tsaro, da kuma abin da ake gani a matsayin nuna son kai na kafafen yada labarai kan Musulmi.
Sanarwar ta ce kafafen yada labarai sun kasa bin ka’idojin gaskiya, adalci da tsaka-tsaki a batutuwan da suka shafi Musulmi.
Majalisar ta kuma soki Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kan tsara zabuka a lokacin Ramadan, tana mai cewa cewa hakan ba abin mamaki ba ne, kuma za su sanya ido sosai tare da sa ran a sake duba lamarin cikin gaggawa.
NSCIA ta bukaci Musulmi su tsaya tsayin daka a kan imaninsu, har ma ta ambato ayar Alkur’ani: inda Allah ke cewa “Inna ma’al ‘usri yusra” ma’ana, “Lalle ne tare da tsanani akwai sauki.”
“Allah yana nufin sauƙi ne a gare ku, ba tsanani ba, domin ku cika adadin kwanakin da aka wajabta, ku kuma girmama Allah bisa shiryar da ku, kuma ko za ku gode.” (Al-Baqarah 2:185)













































