Tinubu ya yabawa Super Eagles duk da rashin lashe gasar AFCON

Tinubu, kasar, Qatar, Najeriya, Legas, kasuwanci
A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Qatar bisa gayyatar Sheikh Tamin Al-Thani sarkin Qatar. Kamar yadda Ajuri Ngelale, mai...

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba tare da karfafa wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles gwiwa bayan wasan da suka buga da Ivory Coast mai masaukin baki wadda ta lashe gasar cin kofin Afirka ta 2023 da aka kammala ranar Lahadi.

Super Eagles sun yi rashin nasara a hannun Ivory Coast da ci biyu da daya, abin da ya kawo musu cikas a kokarin neman lashe kofin karo na hudu.

Karanta wannan: Kano: Hisbah ta kwace kwalaban giya tare da kama mata masu zaman kansu

Duk da rashin nasarar, Shugaba Tinubu ya yaba da jajircewar da Super Eagles suka nuna.

Cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba wa kungiyar saboda kokarin da suka yi a gasar.

Karanta wannan: An ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci yan kasa da kada su duba rashin nasarar da kungiyar ta yi, a maimakon haka su yi murna da nasarorin da Super Eagles ta yi.

A cewarsa, duk da rashin daga kofin a wannan karon, yana da yakinin Super Eagles ta samu babbar nasara a Afirka da duniya da irin kwallon da suka buga a filin wasa.

Ya kara da cewa bai kamata rashin nasarar ta sagar da gwiwoyin jama’a ba, hakan ya zama wani sanadin hada kan al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here