Dandazon ma’aikatan jinya da ungozama ne suka hau titunan birnin tarayyar Abuja domin nuna kin amincewarsu ga wasu sabbin dokoki da hukumar kula da ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa ta shimfida musu.
Sabbin dokokin dai sun hada da kwashe shekaru biyu wadanda suka karanci aikin jinya a jami’a suna aiki a Najeriya kafin hukumar ta tantance su a matsayin kwararrun ma’aikatan jinya. Hukumar ta kuma kara kudin tantancewar daga dubu 29 zuwa dubu 300.
Karanta wannan: Tinubu ya yabawa Super Eagles duk da rashin lashe gasar AFCON
To sai dai kungiyar ma’aikatan jinyar ta ce kudin ya yi yawa kasancewar a cikinsu akwai wadanda suke daukar albashin da bai wuce naira dubu 50 ba a wata.
Ma’aikatan lafiya dai a Najeriya na yawan ficewa daga kasar da zarar sun samu lasisin aiki zuwa wasu kasashen ketare.
Sau da dama dai ma’aikatan lafiya a Najeriya na kokawa kan rashin isasshiyar kulawa da suke samu ciki har da albashi.