Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nadin mukaman mashawarta, nadin ya hada da Nuhu Ribadu a matsayin mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman kan sha’anin tsaro, da wasu guda shida (6)
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban Kasar ya fitar a ranar Alhamis.
Shugaba Tinubu ya nada Mr. Dele Alake a matsayin mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare, yayin da ya nada Mr. Yau Darazo a matsayin mataimaki na musamman kan siyasa da hulda da gwamnatoci.
Sauran mutanen da mukaman da ya nada sun hada da:
- Dr (Mrs.) Salma Ibrahim Anas – Mai ba da shawara na musamman kan Harkar Lafiya.
- Wale Edun – Mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kudi
- Olu Verheijen – Mai ba da shawara ta musamman kan Makamashi
- Zachaeus Adedeji – Mai ba da shawara na musamman kan Kudaden Shiga
- John Ugochukwu Uwajumogu – Mai ba da shawara na musamman kan Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari
Nade naden ya biyo bayan zama da akayi a fadar shugaban kasar dake Aso-Rock, a Abuja.