Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Alake da Wasu 6 a Matsayin Mashawarta

President Bola Tinubu signs
President Bola Tinubu signs

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗa sabbin mashawarta na musamman guda 8.

Wannan naɗe-naɗe na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa, Abiodun Oladunjoye, ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

A cewar sanarwan, sabbin masu bai wa shugaban ƙasa shawaran sun haɗa da;

1. Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru. 2.

2. Ya’u Darazo a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci.

3. Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan tsare-tsare kuɗi.

4. Malam Nuhu Ribaɗo a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tsaro.

5. Misis Olu Verheijen a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan makamashi.

6. Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan tattara haraji. 7. Mista John Ugochukwu Uwajumogu, mai ba da shawara ta musamman kan masana’antu, kasuwanci da hannayen jari.

8. Salma Ibrahim Anas, wacce zata riƙe ofishin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here