Kotun koli taki amincewa da bukatun dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulsalam Sale Abdulkarim A.A Zaura, na dakatar da babbar kotun tarayya daga yi masa shari’a.
Kotun kolin ta kuma umarci dan takarar Sanatan da ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya ta Kano, domin fuskantar tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ke yi masa.
Kotun ta ba da umarnin ta hannun lauyan hukumar ta EFCC, I.G Waru a ranar Alhamis, 24 ga Nuwambar Shekarar 2022.
Hukumar dai tana tuhumar A.A Zaura ne bisa zargin damfarar wani dan kasar Kuwaiti ta hanyar karbar kudi dalar Amurka miliyan 1 da Dubu 320, bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran kasashen Larabawa.
A ranar 9 ga watan Yunin Shekarar 2020, Mai Shari’a Justice Allagoa ya samu wanda ake kara ba shi da laifi kuma ya sallame shi kan dukkan tuhume-tuhumen.
A bisa rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun ta yanke, Lauyan da ke kare masu kara Musa Isah ya daukaka kara a wani yunkuri na soke hukuncin da kotun baya ta yanke.
Sakamakon haka, a wani mataki na bai-daya da wasu mutane uku suka yanke kuma mai shari’a Abdullahi M. Bayero ya yanke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.












































