An kama Mataimakin Shugaban Kasar Malawi bisa zargin karbar cin hancin sama da Dala dubu 280

Vice President of Malawi Saulos Klaus Chilima
Vice President of Malawi Saulos Klaus Chilima

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Malawi ta bayyana cewa, an kama mataimakin shugaban kasar, Saulos Klaus Chilima, tare da tuhumarsa da laifin karbar cin hanci daga wani dan kasuwa dan kasar Burtaniya da ke Malawi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ce, mataimakin shugaban kasar – wanda aka kwace ikonsa ana zarginsa da laifuka da dama da suka hada da cin hanci da rashawa da karbar cin hanci da nufin yin hanyar bada kwangilolin gwamnati ga wadanda suka bashi na goron.

Mai magana da yawun hukumar ta ACB Egrita Mdala, ita ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce “Ya karbi kudaden da suka kai dala 280,000 da sauran kayayyaki daga (dan kasuwan Burtaniya mazaunin Malawi) Zuneth Sattar,” domin sanya kamfanoninsa cikin wadanda za a ba su kwangilolin gwamnatin Malawi.

Hotunan da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna magoya bayan Chilima da ‘yan sanda da alama sun yi taho-mu-gama a lokacin da ake karanta tuhume-tuhumen a gaban kotu.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawar ta yi zargin cewa an ba Chilima tukuicin taimakon kamfanonin Xaviar Limited da Malachitte FZE, da ke da alaka da hamshakin dan kasuwar na Burtaniya Zuneth Sattar.

“A ranar 25 ga Nuwambar shekarar 2022, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawar (ACB) ta kama Dr. Saulos Klaus Chilimaba kan zargin cewa tsakanin watannin Maris zuwa Oktoban shekarar 2021, ya karbi kudaden cin hancin da suka kai dala 280,000 da sauran kayayyaki daga Zuneth Sattar.” in ji ofishin.

A cikin watan Agusta, jaridar Financial Times ta rawaito cewa Sattar na fuskantar bincike daga Hukumar Yaki da Laifuka ta Biritaniya (NCA) kan zargin cin zarafin tsarin sayan jama’a na Malawi.

Ba a tuhume shi da wani laifi ba kuma an hana shi aikata ba daidai ba, in ji Financial Times.

A farkon wannan shekara ne shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya rusa majalisar ministocinsa baki daya bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa ministoci uku masu rike da madafun iko.

Chakwera dai ya yi alkawarin dakile cin hanci da rashawa yayin rantsar da shi a watan Yulin 2020.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here