Sarkin Musulmai kuma shugaban majalisar Ƙoli ta shari’ar musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al’ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga ranar Laraba.
Sultan Abubakar ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata ya fitar da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin shawarwari kan harkokin Musulunci.
Sanarwar ta tunatar da al’umma cewa ranar Laraba, 29 ga watan Dhil-Qa’adah, 1443 wacce ta zo dai-dai da 29 ga watan Yuni, 2022, ita ce ranar farko da ya kamata a duba wata.













































