Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Portugal, sakamakon gayyatar sa da shugaban kasar ta Portugal Marcelo Rebelo de Sousa yayi.
Hakan na nauke cikin wata sanarwa da maitaimakawa shugaban kasar kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar.
Shehu ya kara da cewa Shugaba Buhari zai ziyarci majalisar Portugal ya gana da shugabanta Dr Augusto Santo Silva da Farai Minista na Portugal, Antonio Costa. Ya ce yayin ziyarar, Buhari zai gana da kungiyan yan kasuwan Najeriya mazauna Portugal ya kuma yi wani taron daban da shugabannin kamfanoni da wasu da ake fatan za su saka jari a Najeriya. Buhari, a cewar sanarwar kuma zai hallarci taron United Nations Ocean Conference, wanda aka fara a Lisbon a ranar Litinin 27 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.
Shehu ya ce shugaban kasar zai tattauna da yan Najeriya mazauna Portugal a kan abubuwan da ke damunsu da cigaba a gida Najeriya, ya kara da cewa zai dawo Abuja a ranar Asabar 2 ga watan Yuli.













































