Gwamnatin jihar Kano ta biyawa dalibai 29,031 kudin NECO

Abdullahi Ganduje sabo 1
Abdullahi Ganduje sabo 1

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta biyawa daliban jihar Kano 29, 031 kudin jirrarabawar NECO, ki manin 336 miliyan bana.

Kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ne ya shaidawa manema labarai hakan ranar Litinin a jihar Kano

Yayin da yake maida martini kana rahotanin da ke yawo kan kafafan sada zumunta na zamani cewa daliban jihar Kano bazasu yi jirrabawar NECO ba bana, saboda gazawar gwamnatin gurin biyan kudin jarrabawar.

Garba ya ce wadan da aka biyawa sun hada da dalibai 15,313 wadan da suka sami cin darasu tara a jarrabawar qualifying, da kuma dalibai 1,018 masu bukata ta musaman, mata 7,300, da kuma dalibai 5,400 wadan da kanan hukumumi suka biyawa.

An shaidawa jaridar solacebase cewa hukumar NECO ta sha alwashin  bazata bar daliaban jihar Kano su yi jarrabawar bana ba, sabo da bashin 1.5 biliyan  da ake binta taki biya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here