Gwamnatin jihar Kaduna ta ce dakarun sojin saman Najeriya da ke sintiri ta sama sun kai farmaki wuraren da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da wasu mutane tare da fatattakar ‘yan bindigar da lalata sansanonin su.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Aruwan ya ce jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun gudanar da sintiri ta sama a kan wasu gungun ‘yan bindiga da aka gano a wuraren da ke jihar.
Ya bayyana cewa a yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi, an gudanar da sumame kan wani gungun ‘yan bindiga da aka gano.
“An tabbatar da kashe ‘yan bindiga uku kuma wasu daga cikin wadan da aka yi garkuwa da su sun tsere daga yankin gaba daya, kamar yadda wasu sahihan majiyoyi suka tabbatar.
Ya ce a karamar hukumar Chikun, an gudanar da aikin a kan Faka, Kangon Kadi, Damba, Ungwan Turai, Galbi, Gwagwada da yankuna da dama a karamar hukumar lgabi.
Aruwan ya bayyana cewa an rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da yankunan da ke kusa da su irin su- Buruku, Labi, Udawa, Manini da Polewire har zuwa Kajuru, Jaka da Rabi da Maguzawa.
“Za a ci gaba da sintiri na kasa da na sama a wadannan wurare da sauran wurare,” in ji Aruwan.













































