A yau Alhamis Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar bangare na uku na aikin titin Kano zuwa Maiduguri mai tsohon kilo mita dubu daya da shida da digo dari uku da arba’in da daya, biyo bayan kammala aikin aikin tare ta tabbatar da ingancin sa.
Bangare na uku na aikin ya tashi daga Azare zuwa Potiskum zuwa Bauchi sannan ya tsaya a jihar Yobe.
An yi bikin kaddamar da aikin ne a Azare dake karamar hukumar Katatagum din jihar Bauchi State.
Da yake jawabi a wajen kaddamar aikin Shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya samu wakilcin karamar Ministan ciniki da kasuwanci Maryam Yalwaji-Katagum, ya ce wannan yana daga cikin manyan ayyuka da gwamnatin sa ta dauka da muhimmanci domin amfani da wannan hanya take da shi wajen ci gaban arewacin Nigeria.
Ya kara tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na samar da hanyoyi masu inganci domin saukaka kasuwanci da samar da aikin yi tare da bunkasa harkokin tsaro.













































