Mutum 2 sun mutu a hatsarin da tawagar Mataimakin Gwamnan Sokoto ta yi

Sokoto deputy govs convoy
Sokoto deputy govs convoy

Mutum biyu sun mutu sakamakon hatsarin da ya auku da ya hada da tawagar mataimakin gwamnan jihar Sokoto Muhammad Idris Gobir.

Wadanda suka mutu sune Dan sanda da mai daukar hoto, lokacin da suke komawa babban birnin jihar bayan wata ziyarar aiki da mataimakin gwamnan ya kai sabon Birni.

Karanta wannan: ‘Yan ta’adda sun kara kaiwa hari wasu yankunan Plateau

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar a ranar Laraba ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Mai Magana da yawun rundunar Ahmed Rufa’I, yace hatsarin ya hada da motar dake gaban ta mataimakin gwamnan a cikin tawagar.

Karanta wannan: ‘Yan sandan Kano sun kama wani matashi da ya hallaka Limami

A cewar sanarwar yanzu haka dai sauran wadanda suka sami raunuka yayin hatsarin suna shan magani a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here