A daren ranar Alhamis ne ‘yan ta’adda suka farmaki garin Bundel dake Gundumar Tangur a yankin karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da wasu gungun ‘yan bindiga suka farmaki wasu al’ummu a yankin na karamar hukumar ta Bokkos.
Shuagaban kwamitin wanzar da zaman lafiya na yankin Monday Kassah ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Karanta wannan: Gwamna Namadi ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024
Inda yace ‘yan ta’addar sun farmaki al’ummar garin ne tun a daren ranar alhamis, inda suka kone tare da lalata gidaje da dama.