Duk Da Biyan Su Kudi, SSANU, NASU Sun Ci Gaba Da Yajin Aiki

SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya a ranar Asabar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta saki albashin wata daya ne kawai daga cikin watanni hudu da ta hana.

Ofishin Akanta Janar na Tarayya a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana cewa ya saki albashin da aka hana na ma’aikatan jami’o’in da suka shiga yajin aikin.

Kungiyoyin a karkashin JAC sun fara yajin aikin ne a ranar Litinin din da ta gabata, sakamakon rashin biyansu albashi na watanni hudu, lamarin da ya kai ga rufe harkokin jami’o’in a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here