Wasu dalibai marasa galihu 27 sun bukaci gwamnatin jihar Zamfara da ta biya musu kudin rijistar shiga makarantar koyon aikin lauya ta kasa na zangon 2023/2024.
Bukatar hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar daliban shari’a ta jihar, Mubasshir Umar da Mahmud Sani-Kaura, a Gusau ranar Juma’a.
Karanta wannan: ‘Yan ta’adda sun kara kaiwa hari wasu yankunan Plateau
Ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na daliban ne za su iya biyan makudan kudaden rajistar, don haka akwai bukatar gwamnati ta tallafawa wadanda ba zasu iya biya ba.
Sanarwar ta ce kiran ya zama wajibi don baiwa daliban damar yin rajista kafin cikar wa’adin.
Ta kuma yaba wa gwamnan kan ayyana dokar ta baci a fannin ilimin jihar ta Zamfara.













































