Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandire ta yammacin Africa WAEC tace babu wasu ranakun jarabawarta da suka ci karo dana Jarabawar UTME, wadda hukumar Shirya jarabawar shiga Jami’o’i JAMB ta shirya.
Shugaban hukumar ta WAEC a Najeriya Mista Patrick Areghan, shi ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa Kasa NAN, ranar Asabar a Lagos.
Areghan, ya yi martani ne kan cece-kuce da wasu masu ruwa da tsaki ciki har da iyaye ke yi cewa cin karon ranakun jarabawar ka iya jefa wasu Daliban da zasu rubuta jarrabawar biyu cikin rudani.
Rahotanni sun ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da kwanan watan 5 ga Afrilun 2022, mai taken: Sabunta Jadawalin Jarrabawa ta 2022, wanda aka yiwa daukacin hukumomin da ke kasar, ya nuna an samu sabani a kwanan wata.
Cin karon na ranakun ya kasance ne na jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE), wadda hukumar WAEC ta shirya, da kuma UTME da hukumar JAMB ta shirya.
Areghan ya ce: “Eh, ni ma na gani, amma wannan ranar ba daidai ba ce. “Ina so in tabbatar wa masu ruwa da tsaki da kuma sauran jama’a cewa babu wani abin damuwa saboda babu wani cin karo a ranakun jarrabawarmu da ta UTME, kamar yadda aka gani a cikin Jadawalin da Ma’aikatar ilimi ta fitar.
“Za a fara Jarabawar UTME a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu kuma za a kammala a ranar 14 ga Mayun 2022.
“Yayin da jarabawar WAEC kuma za a fara ta ne a ranar 16 ga watan Mayu ba 6 ga watan ba, kamar yadda ake fada” Inji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa kwafin ingantaccen jaddawalin jarabawar ta WAEC da aka baiwa wakilin NAN din ya tabbatar da cewa ranar 16 ga watan Mayun 2022 za a fara jarabawar.













































